1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Yaki na kara kamari

August 18, 2023

Yakin da ya barke tun watanni hudu da suka wuce a Sudan ya fara bazuwa i zuwa karin wasu yankuna biyu na kasar, lamarin da ke haddasa fargabar samun karuwar 'yan gudun hijira.

Hoto: via REUTERS

Masu aiko da rahotanni sun ce an jiwo karar manyan bindigogi a garin el-Facher hedikwatar Arewacin Darfur, lamarin da ya firgita dubban wadanda suka gudu daga Khartum babban birnin kasar domin neman tudun mun tsira.

Haka ma lamarin ya ke a yankin Nyala inda dakarun RSF masu biyyayya ga janar Mohamed Hamdane Daglo ke ruwan bamabamai ba ji ba gani tare da halaka fararen hula da ba su ji ba su gani ba.

A wani rahoto da jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka fidda, sun zargi dakarun na RSF da cin zarafin kabilun yankunan biyu tare da yi wa mata fyade, lamarin da suka bayyana a matsayin abin damuwa.