1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Yakin Sudan ya dauki hankalin Jaridun Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe
April 19, 2024

Hankulan jaridun Jamus a wannan makon sun karkata ne kan yakin Sudan da kuma yadda nahiyar Turai ta buris da tushen rikicin da kuma hadarin da yakin a Sudan

Südsudan Renk | Sudanesische Flüchtlinge fliehen vor dem Konflikt im Sudan
Hoto: LUIS TATO/AFP

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi hannunka mai sanda game da halin da ake ciki a yakin kasar Sudan, inda ta bayyana cewar nahiyar Turai ta yi buris da tushen rikicin Sudan da ma hatsarin da ke tattare da yaki a wannan kasa. Ta ce Sudan ita ce kasa ta uku mafi girma a Afirka, amma tana kan rugujewa bayan shafe shekara guda ana fada tsakanin sojojin kasar da dakarun rundunar RSF. Miliyoyin mutane sun yi gudun hijira, amma kasashenTurai ba sa la'akari da abin da ke faruwa a wannan kasa.

Jaridar ta ce Turai na kallon yakin a matsayin rikicin cikin gida na nahiyar Afirka, wanda ba shi da wani tasiri ga Turai. Amma wannan ba gaskiya ba ne, a cewar Neue Zürcher Zeitung, saboda rikicin na Sudan zai iya shafar wani yanki mai fama da rikici a Sahel ko Arewacin Afirka da kuma yankin kahon Afirka, lamarin da zai girgiza Turai cikin hanzari saboda za a samu kwararar bakin haure daga Afirka.

'Yan gudun hijirar SudanHoto: Karel Prinsloo/AP/picture alliance

Zeit Online ta mayar da hankali kan matsalar abinci da yankin kahon Afirka a sharhinta mai taken: "Kasashe da dama sun yi alkawarin bayar da tallafin miliyoyi ga Habasha". Jaridar ta ce taron masu ba da agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya tara dala miliyan 610 ga kasar Habasha. Sai dai adadin wannan kudi ya kasance kaso mafi karanci na abin da kasar ke bukata don yaki da 'yunwa. Manufar wannan taron da Birtaniya da Habasha suka shirya, ita ce samar da agajin miliyan dubu na dalar Amurka don magance matsalar abinci da Habasha ke fama da ita.

Zeit Online ta kara da cewa babu sabon alkawari daga Jamus a taron Geneva, inda taimako mafi tsoka ya zo daga Amurka wacce ta bayar da miliyan 154 na Dala, yayin da Burtaniya ke biye mata baya da miliyan 117 na Euro. Ita kuwa Kungiyar EU da kasashe mambobinta sun ce za su samar wa Habasha miliyan 131 na Euro. Sai dai Jamus da ke zama daya daga cikin kasashe da ke ba da taimakon jin kai a duniya, ba ta cikin jerin masu ba da gudummawa, duk da cewa Berlin ta samar da karin kudade a wani taron ba da taimakon Euro miliyan 244 ga Sudan, wacce ita ma mummunar matsalar abinci ta shafa.

Rikicin Gabashin KwangoHoto: Moses Sawasawa/AP/picture alliance

Ita kuwa die tageszeitung ta yi tsokaci ne kan rikicin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar kwango, inda cikin sharhinta mai take "Dakarun sa-kai na Kwango da ake yi wa lakabi da les Patriotes sun zama matsala" ta nunar da cewar sakamakon karuwar tashe-tashen hankula a birnin Goma, sojojin Kwango na tura dakarun sa-kai don agaza wa fararen hula. Jaridar ta ce harbe-harbe na karuwa a Goma babban birnin lardin Kivu ta Arewa da ke gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inda yawan fararen hula da sojoji ko 'yan bindiga suka kashe ko suka azabtar ko suka yi wa fyade na dada karuwa. 

Amma dai die tageszeitung ta nunar da cewar rundunar sojojin Kwango ta girke mafi yawan dakarunta a daukacin yankin Goma. Amma dai ba a biya sojoji da mayakan sa-kai albashi ba na tsawon watanni, kuma da kyar suke samun abin sawa a bakin salati. Sai dai jaridar ta ce 'yan tawayen M23 na cin moriyar matsalar, inda a wata sanarwar da suka fitar suka yi kira ga al’ummar yankin da su tashi su yaki sojojin Tshisekedi.

Hukumar soji ta lardin ta ce a daina barin mayakan Wazalendo suna shigowa cikin birnin Goma da sansanonin ‘yan gudun hijira da makamai.

Sabbin shugabannin Senegal Bassirou Diomaye Faye da Ousmane SonkoHoto: John Wessels/AFP/Getty Images

Za mu karkare da sharhin Frankfurter Allgemeine Zeitung mai taken " Matasan shugabanni a nahiyar Afirka", inda ta ce sauyin mulki da aka samu a kasar Senegal na sa matasa kyautata zato game da makomarsu ko da shi ke ba su fara gani a kasa ba. Jaridar ta ce a Yammaci da Tsakiyar Afirka, tsofaffi na dadewa a kan kujerar mulki bisa goyon bayan kasar Faransa da ta yi musu mulkin mallaka. Amma matasan Afirka da suka kware wajen amfani da kafofin sada zumunta sun daina barin masu shekarun kakanninsu su rinjaye su a siyasance, saboda ba sa samun guraben aiki duk da arzikin mai da gas da kwal da kasashensu suka mallaka.

Amma zuwa sabbin shugabanni irin su Kyaftin Ibrahima Traore a Burkina Faso da kanal Assimi Goita na Mali da Faye da Sonko na Senegal ya juya salon tunani da kamun ludayin shugabancin kasashen Afirka, a cewar Frankfurter Allgemeine Zeitung.