Barazanar karancin abinci a duniya
March 11, 2022Duk da nisan tazarar da ke tsakanin kasashen na Gabas ta Tsakiya da kasar ta Ukraine da Rasha ke ci gaba da yi wa lugudan wuta, masana sun yi amanar cewa, wannan barnar da bama baman na Rasha ke yi, ba za ta tsaya kan kasar ta Ukraine kadai ba harma ga cimakar da ake samarwaa a duniya, musammma ga kasashen Larabawa, wadanda suka dogara ga kasashen na Ukraine da Rasha, wajan samar da kimanin kaso 60% na alkamar da ita ce tushen abinci ga kasashen.
Jalal Yaseer jami,i ne a kwamatin lura da tsaron cimaka na kungiyar kasashen larabawa:
"Kasashen Larabawa na kallon yakin da ya barke a Ukraine cikin halin kaduwa da zulumi da taka-tsantsan, ba don fargabar al,ummominsu, wadanda galibinsu sun dogara ne da alkamar da suke sayewo daga kasashen na Rasha da Ukraine. Don haka duk duniya,kan banda 'yan kasashen biyu, babu wanda zai fi cutuwa da wannan yakin fiye da talakawan Larabawa."
Kamar dai yadda hukumar abinci ta duniya WFP ta yi kashedi, kasashen Yemen da Lebanon da Siriya da Sudan da Tunisiya, wadanda rarar alkamarsu bata wuce ta watanni uku ba, sune za su fi dandana kudarsu. A yayin da kasashen Masar da Maroko da Jodan rarar alkamar da za ta kaisu watanni tara nan gaba, ke da yar dammar gaggauta samawa kansu madadin da ko shakka babu idan har yakin ya jima, hauhauwar farashin cimakar zai kai intaha.
Amr Abdulkuddus na hukumar abincin ta duniya,ya ce idan ba ai tsayuwar daka don tunkarar matsalar ba, kusan galibin kasashen yankin kan iya fuskantar matsalar yunwa:
"Kasashe Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka kan iya fadawa cikin tamowa. Wadanda za su iya tsallake wannan siradin su ne kasashen da ke da arzikin makamashi, wadanda tashinsa a duniya zai iya taimaka musu cike gibin da tashin farashin da alkamar zai haifar a kasafin kudinsu."
A yanzu dai kasashen Switzland da Kanada ne za su iya zama madadin da za su iya samarwa kasashen na Larabawa alkama, wadanda tuni suka ninka farashinta.
Sausan Kablawi, wata mai fafutuka 'yar kasar Tunisiya, ta ce yakin na Ukraine ya kunyata shuwagabannin kasashensu:
"Shugabanninmu sun bamu kunya da suka gaza wajan samar da alal misali akalla burodin da talaka zai ci. Duk kuwa da fadin kasar nomar da kasashenmu ke dasu da yakai mu ciyar da duniya baki daya.Ba abun da suka iya kan banda danne talakawansu da zama 'yan amshin shatan kasashen ketare."
Tuni dai talakawan na kasashen yankin suka fara kokawa da wannan matsalar:
"Me ya rage ba su raba talakawa da shi ba. Hatta gurasar da zamu sa a bakin salati ta gagare mu. Wannan wace irin rayuwa ce?"
Kadan ana iya tunawa dai, tsadar burodi, ya yi sanadiyar faduwar tarin gwamnatocin mutu kan raba a yankin, lamarin da ake fargabar maimaituwarsa, muddin yakin na Ukraine ya tsawaita.