1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Putin ya yi barazanar kai hare-hare kan kasashen Turai

Abdourahamane Hassane
November 22, 2024

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya bayyana taikaicinsa bayan da Rasha ta harba makami mai linzami mai cin dogon zango kan Ukraine wanda ke dauke da sinadarin nukiliya OGIV.

Hoto: Vyacheslav Prokofyev/Sputnik/Kreml Pool/AP/picture alliance

Shugaban gwamnatin  Jamus   ya yi kiran da a yi taka tsan-tsan a tallafin makamai da kasashen yamma ke bai wa Ukraine. Shugaba Vladimir Putin ya ce a yanzu yaki na Ukraine na kan hanyar zama yakin duniya, kuma ya yi gargadin cewar bai kawar da kai hare-hare ba kan kasashen yammacin Turai. Kungiyar tsaro ta NATO da Ukraine za su gana a ranar Talata a Brussels don tattaunawa kan harba makami mai linzami da Rasha ta yi , kamar yadda  majiyoyin diflomasiyya  suka sanar.