1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Yakin Ukraine ya sa mutane miliyan 14 yin hijira

February 22, 2024

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa kimanin 'yan Ukraine miliyan 14 ne suka tsere daga matsugunensu sakamakon mamayar Rasha.

Russischer Angriffskrieg gegen die Ukraine
Hoto: Narciso Contreras/Anadolu/picture alliance

Baya ga wannan adadi da ke wakiltar kashi daya cikin uku na al'ummar Ukraine da suka nemi mafaka a kasashe 11 na nahiyar Turai, da akwai karin wasu miliyan 3,7 da su kuma suka watsu a wasu sanssan kasar.

A lokacin da take sanar da wadanan alkaluma shugabar hukumar Amy Pope ta ce kawo yanzu mutane miliyan 4,5 sun koma gida bayan lafawar lamura a yankunansu, sai dai amma suna bukatar tallafi domin sake gina rayuwarsu. Manyan bukacin tsaffin 'yan gudun hijirar in ji Mme Pope sun hadar da guraren zama da kuma ababen more rayuwa.