Yammacin Afirka: Sabuwar hanyar shiga Turai
August 26, 2024Firimiyan Sipaniyan zai yi ziyarar ne a kasashen Mauritaniya, Senegal da Gambiya, wandanda ke bakin ruwan da bakin haure ke bi don tsallakawa daga Afirka izuwa Turai. Wannan dai ita ce ziyara ta biyu a bana da Pedro Sanchez ke kaiwa a Yammacin Afirka, wanda kuma ziyara ce da duk ke kokarin magance matsalar 'yan gudun hijira. Yayinda a da bakin haure ke ta bin kasar Libiya su shiga Turari ta kasar Italiya, amma a yanzu sakamakon yunkurin kasashen Turai na karfafa toshe hanyoyin da 'yan gudun hijiran suka saba bi, a yanzu sai ku bullo da hanyar shiga Turai ta tsibirin Canary. 'Y gudun hijiran dai kan tashi musamman daga gabar ruwan kashen Senegal da Maurtaniya. A cewar rundunar Frontex da ke tsaron gabar ruwan Turai, rundunar da aka kafa don hana bakin haure shiga Turai, tace a watannin bakwai na farkon bana kadai kimanin baki 'yan ci-rani 21,620 suka tsallaka daga gabar ruwayen Afirka izuwa Tsibirin Canary da ke karkashin kasar Spain.