1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Turmutsitsi ya halaka Kiristoci a Laberiya

January 20, 2022

An yi turereniyar a wani filin kwallo da ke a wajen birnin Monrovia a yayin wani taron addu'a  da aka fi sani da ''crusade'' a Laberiyar.

Liberia George Weah als Präsident vereidigt
Hoto: Reuters/T. Gouegnon

Wani turmutsitsin mabiya addinin Kirista a Laberiya ya yi ajalin mutane akalla 29. Kafofin yada labaran kasar sun ce lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba wayar garin Alhamis din nan. 

Kawo yanzu babu cikakken bayani a kan yadda yamutsin ya yi sanadiyyar mutuwar masu ibadar. To amma 'yan sanda sun ce akwai yiwuwar adadin mutanen da lamarin ya halaka sun haura 29.