Yamutsin siyasa a Yamen
January 19, 2015Talla
Rahotanni daga kasar Yemen na cewa ana can ana gumurzu tsakanin sojin kasar da mayakan Huthi. kamar dai yadda kamfanin dillancin labaran Faransa wato AFP ya labarta, a halin da ake ciki mayakan na Huthi da ake alakantawa da mabiya darikar Shi'a ne, na ikirarin karbe iko da sansanin soji dake kula da fadar shugaban kasan.
Ministar yada labaran kasar ta Yamen Nadiya Al-saqaf, ta danganta wannan harin da yunkuri na kifar da gwamnatin kasar. An dai tabbatar da mutuwar mutum guda, sai dai ba a bayyana bangaren da ake zargi da yunkurin na kifar da gwamnati ba. Tun watan Satumba ne dai 'yan tawayen Huthi suka kame wani bangaren Sana'a babban birnin kasar ta Yamen.
Mawallafi: Muntaqa Ahiwa
Edita: Usman Shehu Usman