1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan fursunoni sun yi a birnin Yawande na kasar Kameru

Suleiman Babayo
July 23, 2019

'Yan fursuna sun yi yamutsi a Yawande babban birnin kasar Kameru domin nuna takaicin yanayin da suke ciki inda galibi suka fito daga yankin da ake magana da harshen Ingilishi da ake samu 'yan aware masu dauke da makamai.

Kamerun | Unterstützer anglophoner Aktivisten aus Gefängnis entlassen
Hoto: Reuters/Stringer

A birnin Yawunde na kasar Kameru daruruwan fursunoni sun yi bore a inda ake tsare da su a gidan yarin da ake kira Kondengui. Gwamnati ta tura daruruwan sojoji tare da tabbatar da kara matakan tsaro, domin dakile matsalar inda galibin mutanen da suke tsare an kama su daga yankin da ake magana da harshen Ingilishi da ke samun 'yan aware masu tayar da kayan baya.

Babu karin bayani game da abin da ya faru daga bangaren gwamnatin kasar ta Kameru.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW