’Yan Ƙungiyar Taliban sun kashe sojojin Birtaniya guda biyu a Afghanistan.
July 2, 2006Hukumar rundunar sojin Birtaniya ta tabbatad da rahotannin cewa, wasu sojojinta biyu sun sheƙa lahira a ƙasar Afghanistan, yayin da mayaƙan ƙungiyar Taliban suka kai musu hari a sansaninsu da ke kudancin ƙasar. Rahotannin da muka samu sun ce, harin ya auku ne a cikin daren jiya a lardin Sangin da ke jihar Helmand. Wani tafintan sojojin, ɗan ƙasar Afghanistan, shi ma ya rasa ransa a harin. Da yake yi wa maneman labarai jawabi a birnin Kabul game da harin, wani kakakin sojin Birtaniya a Afghanistan, Kyaftin Drew Gibson, ya ce ’yan Taliban sun afka wa sansanin ne da ƙananan makamai da kuma rokokin gurnat. Sojoji 4 ne kuma suka ji rauni, waɗanda a halin yanzu ake yi musu jiyya a asibiti, inji kakakin. Sakataren tsaron Birtaniya, Des Browne, ya yi juyayin mutuwar sojojin, amma ya ce kamata ya yi Birtaniya ta nuna wa ’yan Taliban ɗin abin da ya kira matuƙarsu, saboda kamar yadda ya bayyanar, mutane ne masu adawa da ci gaban ƙasar ta Afghanistan.