1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan adawa sun bukaci saka lokacin zabe

Suleiman Babayo AH
February 21, 2024

'Yan adawa na kasar Senegal da ke neman shugabancin kasar sun zargi hukumomi da tsaiko wajen saka lokacin gudanar da zaben shugaban kasar da kotun tsarin mulki ta soke matakin jinkirtawa na tsawon watanni 10.

Senegal, Dakar | Shugaba Macky Sall na Senegal
Shugaba Macky Sall na SenegalHoto: Sylvain Cherkaoui/AP/picture alliance

A makon jiya Shugaba Macky Sall na kasar Senegal ya yi alkawarin biyayya ga hukuncin kotun wajen saka lokacin zaben nan gaba kadan. Ita dai kotun tsarin mulki ta yi watsi da dokar da shugaban kasar ya dauka na jinkirta zaben da aka tsara ranar 25 ga wannan wata na Febrairu har zuwa karshen shekarar.

Karin Bayani: Rikicin siyasar Senegal

Yanzu tilas Shugaba Sall ya saka lokacin zaben gabanin karewar wa'adin mulkinsa ranar 2 ga watan Afrilu, abin da 'yan adawa suke ganin kamar ana jan kafa wajen saka lokacin. Ita dai kasar Senegal ta kasance kasa daya da sojoji ba su taba kwace madafun iko ba a yankin yammacin Afirka.