1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa ba za su iya ka da Wade ba

February 26, 2012

Kimanin 'yan Senegal miliyan biyar ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa dake tattare da taƙaddama.

Senegal's incumbent President Abdoulaye Wade attends an election campaign rally in the capital Dakar February 22, 2012. Senegalese are due to vote in presidential elections on Sunday amid rising violence during protests against Wade's decision to run for a third term in contravention of constitutional limits. REUTERS/Joe Penney (SENEGAL - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: REUTERS

A zaɓen shugaban ƙasar Senegal, masu kaɗa ƙuri'a kimanin miliyan biyar za su zaɓi ɗaya daga cikin 'yan takara 15. Sai dai tashe-tashen hankula sun mamaye halin da ake ciki a wannan ƙasa da kawo yanzu ake da kwanciyar hankali da lumana. 'Yan adawa da wani ɓangare na jama'a sun yi ta gudanar da zanga-zangar nuna adawa da sake tsayawa takarar shugaba Abdoulaye Wade. A shekarar 2000 lokacin da Wade ɗin ya hau kan karagar mulki bayan shekaru gommai yana adawa, an yi farin ciki matuƙa amma yanzu shekaru 12 baya farin jininsa ya dushe.

Thiat mawaƙi da ya ƙirƙiro wata ƙungiyar matasa masu bore da ake wa laƙabi da "Ya kai mana iya wuya", yake cewa: "Mafarkin abin tsoro, shekaru 12 bai taɓuka komai ba. Lokaci ya yi da 'yan Senegal za su farka daga barci."

Thiat ba ya shiru idan ana maganar sukar lamirin shugaba Abdoulaye Wade ne. Akwai mabambamtan ra'ayoyi game da ayyukan da shugaban yayi wa ƙasar. A wasu yankunan ƙasar an samu ingantuwar ababan more rayuwa, sannan hukumomi kuɗi na duniya sun ce tattalin arzikin ƙasar yana da kyau. Sai dai abin da ke ɓata wa ƙungiyar matasan da ɗaukacin talakawa rai shi ne sake tsayawa takarar Wade wanda shi da kansa ne ya ƙayyade wa'adin shugabancin ƙasar ya zuwa biyu. Fadel Barro memba ne na ƙungiyar, ya ce matakin yin tazarce na Wade ya saɓa da kundin tsarin mulkin ƙasa.

Fafatikar girke sahihiyar demokraɗiya

"Koma-baya ce ga demokraɗiyya. Idan muka ƙyale shi hakan ya zama wani somin-taɓi. Gwagwarmaya muke ta girƙe demkraɗiyya, ba wai saboda yawan shekarun Wade ba, sai saboda take-takensa na neman tilasta ɗansa akanmu."

Wannan na daga cikin sukar da ake wa Wade wato na neman kafa wata daular mulkin mulukiya wato ɗansa ya gaje shi. Ko da yake kakakin shugaban Amadou Sall ya musanta haka, amma gaskiya ita ce a shekarar 2011 Wade ya so a yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima ta yadda za a zaɓi shugaba da mataimakinsa a lokaci guda, kuma daga bisani ana iya maye gurbin mataimakin da zarar shugaban ƙasa yayi murabus. 'Yan Senegal dai sun yi fatali da wannan dabara ta siyasa.

Ɗan takarar adawa Idrissa Seck bai gabatar da wani kyakkyawan shiri baHoto: REUTERS

Su ma 'yan adawa sun yi amfani da wannan damar don yin fatali da gyarar da aka yi wa tsarin mulkin. Kasancewa sun ƙaurace wa zaɓen 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a shekarar 2009 saboda zargin tabƙa maguɗi, ba su da wakilci a majalisun ƙasar.

Rashin kyakkyawan shirin shiga zaɓe

Werner Nowak shi ne daraktan gidauniyar Friedrich-Naumann a birnin Dakar yayi ƙarin haske.

"'Yan adawa suka jawo wa kansu koma baya domin a hukumace ba su da wata kafa ko ɗaya da za su ƙarfafa matsayinsu a siyasance. Sai dai su hau kan titi su yi zanga-zanga."

Da yawa daga cikin 'yan Senegal na ganin ƙungiyar nan ta M 23 da aka kafa a tsakiyar watan Mayun 2011 da nufin haɗa ƙarfi wajen tinkarar shugaba Wade ba za ta iya yin wani kataɓus ba. Duk da cewa suna musanta cewa akwai rarrabuwar kawuna tsakanin, amma su kansu 'yan adawa ba su da wata alƙibla ta siyasa, in ban da cewa za su yaƙi cin hanci da rashawa da samar da ababan more rayuwa. Mouhamadou Mbodj wakilin ƙungiyar Transparency International a Dakar ya soki lamirin 'yan adawa da cewa.

Jama'a za ta ci-gaba da zanga-zanga har sai Baba ta ganiHoto: dapd

"Ba su gabatar da wani shiri takamamme ba. 'Yan takara Idrissa Seck da Macky Sall sun gabatar da manufofinsu amma ba su ƙunshi wani sahihin shiri na zaɓe ba."

Boren 'yan adawa dai ya tsaya ne a Dakar babban birnin ƙasar, amma ƙungiyoyin jama'a sun ce ba za su saduda ba, idan Wade yayi nasara ba za su bari Wade ya yi mulki ba ko da za su ci-gaba da zanga-zanga har si sun ga abin da ya ture wa buzu naɗi.

Mawallafa: Dirke Köpp/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadisou Madobi