1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa na kokawa kan lafiyar Buhari

February 7, 2017

Bisa dukkan alamu har yanzu akwai sauran tafiya a kokarin da fadar gwamnatin Najeriya ke yi na kwantarwa da 'yan kasar hankali kan hakikanin halinda shugaban su ke ciki.

Paris Medef Zentrale Buhari Gattaz
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Getty Images/AFP/E. Piermont

Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osibanjo ya bayyana cewa ya tattauna da mai gidansa Buhari, duk dai da nufin kwantar da hankulan 'yan kasar da ke tunanin da biyu a cikin halin rashin lafiyar da shugaban ke ciki.

To sai dai kuma daga dukkan alamu har zuwa yanzu an gaza kaiwa ga burge 'yan siyasar kasar walau cikin jamíyyar APC mai mulki ko kuma 'yan PDP dake zama babbar Jam'iyyar adawa a kasar.

Hoto: DW/K. Gänsler

Gaza samar da bayanai game da nau'ín rashin lafiyar shugaban da rashin sanin ranar kamun aikin nasa dai, na cigaba da jefa tunani daban daban a zukatan 'yan siyasar dake cewar ana kokarin boye zahiri akan rashin lafiyar ta Buharin ga yan kasar.

Sabo Imam Gashua dan jamíyyar APC mai mulki da kuma ya ce sannu a hankali, jamíyyar tasa na daukar salo irin na jam'iyyar PDP ta adawa can baya wajen rufa rufar  bayanan da ya kamaci 'yan kasar su sa ni.

''Kokarin sauyin  tsarin mulki ko kuma kokari na boye bayanai,a baya dai PDP ta share tsawon  lokaci tana kokarin boye halin da  marigayi Umar Musa yar Adua ya ke ciki kafin daga baya ya kai ga rasuwa a shekara ta 2010''.

Hoto: DW/S. Olukoya

To sai dai kuma a fadar Dr.Umar Ardo dake zaman 'dan Jam'iyyar PDP lallai akwai darasi babba ga yanda mashawartan  Buhari ke kokarin wasa da hankalin 'yan kasar cikin batun na lafiyar Buhari.Abun jira a gani dai na zaman hango fitila ta shugaban cikin kasar,dake yanayi maras kyau kuma ke bukatar ingantaccen jagora yanzu.