1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa na murnar rusa zaben Kenya

Mohammad Nasiru Awal ARH
September 1, 2017

Kotun kolin kasar ta soke sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Agusta bayan bankado kurakurai, wanda ya nuna shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta ne ya lashe.

Kenia Präsidentschaftswahl Jubel Anhänger Uhuru Kenyatta
'Yan adawa a kasar Kenya ke nan ke nuna jin dadin soke zaben shugaban kasaHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Kotun ta ce ta gano cewa an tafka kurakurai, saboda haka ta ba da umarnin a sake sabon zabe cikin kwana 60 masu zuwa. Babban alkali Justice David Maraga ya ce: "mun ayyana wannan zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar takwas ga watan Agustan 2017, a matsayin wanda ba a gudanar bisa kundin tsarin dokar kasa ba, wanda hakan ya sa muka soke shi baki daya."

Da ma tun farko dan takarar jam'iyyar adawa Raila Odinga ya yi korafin cewar an tabka magudi ta hanyar yin kutse cikin na'urar hukumar zaben kasar, lamarin da ya sa ya garzaya kotu, kuma ya samu nasara da ya bayyana ta da wata nasara ga demokaradiyya a nahiyar Afirka.

Dan takarar shugaban kasar Kenya Raila OdingaHoto: Reuters/S. Modola

"Hakika wannan rana ce mai cike da tarihi ga al'ummar kasar Kenya da ma al'ummomi nahiyar Afirka gaba daya. A karon farko cikin tarihin demokaradiyyar Afirka, kotu ta yanke hukuncin soke wani zaben shugababn kasa mai cike da kura-kurai."

Sai dai a martanin da ya mayar dangane da hukuncin kotun kolin, shugaba Uhuru Kenyatta ya yi kira ga al'ummar Kenya da su zauna lafiya da juna. Ya ce ko da yake bai yarda da hukuncin ba, amma ya mutunta shi, amma ya soki lamirin alkalan kotun ya ce mutum shida sun yanke hukuncin adawa da zabin da al'umma ta yi.

Shugaban kasar Kenya Uhuru KenyataHoto: Reuters/T. Mukoya

Ya ce: "Yana da muhimmanci mu 'yan Kenya mu girmama dokar kasa. Ni kam ban yarda da hukuncin da aka ayyana a wannan Juma'a ba, amma ina gimama shi kamar yadda nake kin shi. Domin kamar yadda na fada, miliyoyin 'yan Kenya sun yi layi, sun zabin abi da suke so, amma mutane shida sun ki wannan zabi na al'umma." 

A dai halin da ake ciki 'yan adawar kasar ta Kenya sun nuna bukatar hukunta dukkan jami'an hukumar zaben da aka same su da laifin aikata ba daidai ba, kamar yadda mataimakin shugaban kawancen 'yan adawa Musalia Mudavadi ya nunar a wata hira ta musamman da tashar DW.

Ya ce: "Mun yi farin ciki, hukunci ya tabbatar da korafe-korafen da muka ta yi cewa an tabka magudi a zaben, kana hukumar zabe ta yaudari masu sa ido a zaben na kasa da kasa wajen ba su bayanai na bogi. Ba su bi dokokin kundin tsarin mulki ba. Gaskiya ya kamata a tuhumi wasunsu da aikata laifi."

Shugaban hukumar zaben Kenya Wafula ChebukatiHoto: picture-alliance/AP Photo/S. A. Azim

Bisa ga dukkan alamu dai hukumar zaben ta Kenya ta ji wannan bukata ta 'yan adawa inda tuni shugaban hukumar zaben, Wafula Chebukati, ya yi kira ga ofishin mai shigar da da ya gaggauta yin bincike tare da hukunta dukkan jami'an hukumar da suka saba wa dokar zabe. Ya ce hukumar za ta aiwatar da hukuncin kotun na soke zabe. Ya ce: "Hukumar na sane da karancin lokaci na sake shirya zaben shugaban kasa karkashin dokokin tsarin mulki da dokokin zabe. Muna kira ga kotun da ta yi mana cikakken bayani don mu gane wurare da za mu mayar da hankali kai a daidai lokacin da muke tsara lokacin gudanar da sabon zaben shugaban kasa."

Wannan dai shi ne karon farko da aka yi zaben shugaban kasa a kasar ta Kenya da ke zama cibiyar tattalin arziki Gabashin Afirka.