1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan adawa sun gudanar da gangamin kyamar gwamnati a Angola

November 23, 2024

Dubun dubatar mutane suka gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a Luanda babban birnin Angola domin nuna adawa da gwamnatin da aka kafa a kasar tun a shekara ta 2022.

Magoya bayan jam'iyyar UNITA a kasar Angola a yayin da suke gudanar da zanga-zanga karkashin jagorancin madugun adawa Adalberto Costa Júnior
Magoya bayan jam'iyyar UNITA a kasar Angola a yayin da suke gudanar da zanga-zanga karkashin jagorancin madugun adawa Adalberto Costa JúniorHoto: Borralho Ndomba/DW

Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ce jami'an 'yan sanda sun yiwa masu zanga-zangar kawanya domin kwantar da tarzoma tare kuma da tabbatar da doka da oda, duk da cewa  masu gangamin sama da dubu 4,000 sun yi dafifi a birnin na Luanda ba tare da hargitsi ba, inda suke ci gaba da sukar jam'iyya mai mulki ta People's Movement for the Liberation of Angola (MPLA) da kuma shugaban kasar Joao Lourenco.

Karin bayani: Angola ta yanke shawarar ficewa daga kungiyar kasashe masu arzikin man fetur

Babbar jam'iyyar adawar kasar UNITA ita ce ta kira gangamin wacce kuma a baya ta shigar da kara kotu domin kalubalantar nasarar jam'iyya mai mulki, yayin da daga bisani kotun kolin kasar ta yi watsi da karar.

Karin bayani: Angola: Ina kadarorin da aka kwato na Isabel dos Santos?

Sakataren Jam'iyyar UNITA wacce a baya ta kasance kungiyar 'yan tawaye kafin ta rikide zuwa jam'iyya, Alvaro Chikwamanga ya shaida wa AFP cewa sun fito gangamin ne domin nuna fushinsu kan yadda ake gudanar da mulkin kama-karya a kasar.