1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

'Yan adawa sun kira zanga-zanga a Venezuela

August 18, 2024

Dubun dubatar 'yan adawa sun yi cincinrindo a birnin Caracas na Venezuela domin nuna adawa da sakamakon zaben shugaban kasar wanda ya sake bawa shugaba mai ci Nicolas Maduro, damar kasancewa akan karagar mulki.

Masu zanga-zanga a birnin Caracas na Venezuela
Masu zanga-zanga a birnin Caracas na Venezuela Hoto: Gaby Oraa/REUTERS

Dubban masu zanga-zanga na gudanar da gangami a biranen kasar da kuma wasu kasashen da ke goyon bayan fafutukar da suke yi musamman Spain da Belgium da kuma Australia, bisa kiran da jagorar adawar kasar Maria Corina Machado ta yi na gudanar zanga-zangar gama-gari har sai abin da hali ya yi.

Karin bayani: EU za ta dauki mataki kan shugaban Venezuela

Machado ta shiga sahun 'yan zanga-zangar domin tursasawa shugaba Maduru sauka daga kan karagar mulki tare da jaddada cewa magudi aka tafka a zaben shugaban kasar da a cewar 'yan adawan 'dan takararsu  Edmundo Gonzalez Urrutia, shi ne ya lashe zaben.

Karin bayani: Har yanzu tsugune bata kare ba a kasar Venezuela

Dambarwar siyasar Venezuela ta samo asali tun bayan da Hukumar Zaben Kasar ta tabbatar da Nicolas Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 52 bisa 100 wanda hakan zai bashi damar ci gaba da kasancewa akan mulki har zuwa 2031, kazalika  Hukumar ba ta yi cikakken bayani ba akan sakamakon zaben, abin da 'yan adawan ke cewa su suka yi nasara.