1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

'Yan adawa sun lashe zaben yankin Kashmir a kasar Indiya

Mouhamadou Awal Balarabe
October 8, 2024

Sakamakon zabe ya nuna cewa jam'iyun da ke kawancen NC sun samu akalla kujeru 46 daga cikin 90 na 'yan majalisar dokokin kashmir, yayin da jam'iyyar BJP ta Firaministan Indiya Narendra Modi ta samu kujeru 27.

Shugabannin kawancen NC sun yi alkawarin inganta halin rayuwar 'yan Kashmir
Shugabannin kawancen NC sun yi alkawarin inganta halin rayuwar 'yan KashmirHoto: DW

Jam'iyyun adawa sun lashe zaben yankin Kashmir da ke fama da rikici a Indiya, shekaru biyar bayan da gwamnatin tarayya ta sanya shi karkashin kulawarta. Sakamakon da hukumar zaben ta fitar, ya nuna cewa jam'iyun da ke karkashin kawancen NC sun samu akalla kujeru 46 daga cikin 90 na 'yan majalisar dokokin yankin, lamarin da ke ba su damar kafa gwamnatinta, yayin da jam'iyyar BJP ta Narendra Modi ta samu kujeru 27.

Karin bayani: Jam'iyyar BJP a Indiya na son jan hankalin Musulmi a Kashmir

 An dai shafe kwanaki uku ana gudanar da zaben da ke zama na farko a cikin shekaru goma, wanda yake shaidar da bukatar 'yancin cin gashin a Khasmir. Tun dai shekaru biyar da suka gabata ne Firaministan Narendra Modi da ke bin tafarkin Hindu ya soke matsayin 'yancin cin gashin kai na yankin Kaashmir da ke da rinjayen Musulmi, tare da tura sojoji da kuma nada kantoma. Ko da a  lokacin yakin neman zabe, sai da Firimiya Mista Modi ya yi alfahari da dawo da tsaro da farfado da tattalin arzikin yankin. Amma shugannin adawa suka ce wannan nasarar da suka samu a zabe na ba su damar tafiyar da yankinsu a kan tafarkin siyasarsu.