1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa a Burundi sun dauki sabon salo

Yusuf BalaJune 9, 2015

A cewar mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Burundi Willy Nyamitwe, yadda 'yan adawar suka yi kunnen uwar shegu da bukatar Majalisar alama ce ta rashin mutuntawa.

Burundi Oppositioneller festgenommen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Delay

Kungiyoyin fafutika a kasar Burundi a ranar Talatan nan sun yi fatali da bukatar mai shiga tsakaninsu da bangaren gwamnati daga Majalisar Dinkin Duniya, inda suka bayyana shi da cewa take-takensa sun nuna alamun goyon bayan shugaba Pierre Nkurunziza mai muradin yin tazarce a karo na uku.

Kungiyoyi masu fafutika da dama sun tura wasika zuwa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, inda cikin wasikar suka ce mai shiga tsakanin daga kasar Aljeriya Said Djinnit, suna da tantama kan aikinsa a cewar Pierre Claver Mbonimpa, da ke gaba-gaba cikin masu adawa da tazarcen na shugaba Nkrunziza.

A cewar mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Burundi Willy Nyamitwe, yadda 'yan adawar suka ki mutunta bukatar ta jami'in diplomasiya Djinnit, alama ce ta rashin nuna dattako