1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan adawa sun yi watsi da dage zaben Senegal

February 4, 2024

'Yan adawa a Senegal sun yi watsi da matakin dage zaben kasar na ranar 25 ga watan Fabarairu, tare da kiran magoya bayansu da su fito zanga-zanga a birnin Dakar fadar gwamnati.

'Yan adawa sun yi watsi da dage zaben Senegal
'Yan adawa sun yi watsi da dage zaben SenegalHoto: John Wessels/AFP

Shugabannin jam'iyyun adawa da dama a Senegalsun ce za su kaddamar da yankin neman zabe kamar yadda aka tsara a can baya, kana kuma za su ci gaba da bijerewa matakin da shugaba mai barin gado Macky Sall ya dauka a ranar Asabar wanda ke karo na farko tun bayan shekarar 1963.

Karin bayani: Senegal: Shugaba Sall ya dage zabe

Daga cikin wadanda suka yi fatali da matakin dage zaben har da fitaccen dan adawa Khalifa Sall, da kuma tsohuwar firaminstar kasar Aminata Touré. Dukanninsu sun isar da kiraye-kiraye na a fito zanga-zanga a ranar Lahadi (04.02.2024) domin ceto kasar daga ta'addancin dimukuradiyya. 

Tun dai bayan sanar da dage zaben har sai baba ta gani, kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika ECOWAS da ma'aikatar harkokin wajen Amurka suka bayyana damuwa tare da kira da a gaggauta sake tsayar da sabuwar rana da sharuddan gudanar da zabe sahihi cikin 'yanci da adalci.