1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan adawa sun yi zargin tafka magudi a zaben kasar Mozambik

October 16, 2024

Kamar yadda aka yi hasashe, jam'iyya mai mulki a Mozambik ta FRELIMO ta lashe zaben da ya gudana a kasar. Sai dai 'yan adawa sun bayar da rahotannin mummunan magudi, lamarin da ya sa masu sanya idanu sun bayyana damuwa.

Manuel de Araujo na RENAMO ya ce yana da tabbacin an yi magudin zaben Mozambik
Manuel de Araujo na RENAMO ya ce yana da tabbacin an yi magudin zaben MozambikHoto: Marcelino Mueia/DW

Ga dukkan alamu, jam'iyyar FRELIMO da ke mulki tun bayan samun 'yancin kan kasar Mozambik tun shekaru 50 suka gabata da dan takararta Daniel Chapo za su yi nasara. Venancio Mondlane ya zo na biyu a zaben, kuma daya daga cikin 'yan adawa uku, kana wanda ya fice daga cikin babbar jam'iyyar adawa ta RENAMO kuma ya goga da dan takarar jam'iyyar Ossufo Momade. Sai dai tuni Venancio Mondlane ya yi ikirarin lashe zaben na shugabancin kasar Mozambik,  inda ya yi zargin tafka magudi. Hukumar zaben kasar ta bayyana sakamakon farko na zaben da ya tabbatar da jam'iyya mai mulki ta Frelimo a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasar. Ana Chemane, da ke magana da yawun hukumar na cewa: "Daniel Francisco Chapo, ya samu kaso 53,68% na kuri'u yayin Venâncio António Bila Mondlane, ke da kaso 33,84%." 

Karin bayani: Kalubalen sabuwar gwamnatin Mozambik

Daniel Chapo na jam'iyyar FRELIMO na kan hanyar zama shugaban kasar MozambikHoto: ALFREDO ZUNIGA/AFP/Getty Images

Wannan ya nuna cewar Daniel Chapo na jam'iyyar FRELIMO zai zama shugaban kasa na gaba, inda zai daura kan mulkin da jam'iyyar ta yi na tsawon shekaru 50. Yayin da Venâncio Mondlane ke matsayi na biyu da kaso 33.84%, a matsayi na uku akwai jam'iyyar Renamo inda dan takararta Ossufo Momade mai kaso 9%, sai mutum na hudu a zaben Lutero Simango na jam'iyyar MDM mai kaso uku cikin 100. António Niquice, sakataren na jam'iyyar FRELIMO a birnin Maputo fadar gwamnatin kasar ya nuna gamsuwarsa, inda ya ce: "Wannan sakamako ne da ya nuna abin da mutane suka zaba. An yi zabukan cikin gaskiya da adalci."

Karin bayani:Yankin arewacin Mozambik na fama da matsalar tsaro

A yankin Cabo Delgado na Arewa maso gabashin kasar Mozambik mai fama tashe-tashen hankula na 'yan jihadi tun shekara ta 2017, dan takarar jam'iyyar mai mulki FRELIMO, Daniel Chapo ne ya lashe yankin da kaso 66 cikin 100, yayin da Venancio Mondlane ya kasance a matsayi na biyu da kaso 22 cikin 100 na kuri'un, inda Ossufo Momade yake kasance a matsayi na uku, sannan Lutero Simango yake mataki na karshe.  Jaime Guiliche mai sharhi ne kan lamuran siyasar kasar ta Mozambik ya ce: " Muna cikin yanyin da jam'iyyar RENAMO ta gaza kasancewa a matsayi na biyu, abin da ya rage tasirin jam'iyyar. Haka zai sauya taswirar siyasar kasarmu." 

Karin bayani:Babban zabe a Mozambik

'Yan Jam'iyyar RENAMO suka ce kasar Zimbabuwe ta yi katsalandan a zaben MozambikHoto: Bernardo Jaquete/DW

Ita dai jam'iyyar RENAMO ta fafata yakin basasa na tsawon shekaru lokacin da jam'iyyar FRELIMO ta yi kane-kane kan madafun ikon kasar ta Mozambik. 'Yan adawa sun yi zargin tafka magudi musamman daga kasar Zimbabuwe saboda dangantakar da ke tsakanin jam'iyyar Zanu-PF mai mulkin Zimbabwe da kuma jam'iyyar FRELIMO mai mulkin kasar ta Mozambik. Wata jaridar Zimbabuwe ta yi zargin yadda dubban magoya bayan jam'iyyar Zanu-PF suka tsallaka zuwa Mozambik domin tabbatar da kada kuri'un domin jam'iyyar FRELIMO ta samu nasara a zaben na Mozambik da ya gabata.