1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan adawa suna kara shiga zaben Kamaru

Zakari Sadou SB
July 21, 2025

Jam'iyyar MANIDEM ta Anicet Ekane ta tsayar da Maurice Kamto a matsayin dan takara na zaben shugaban kasa na 2025 al'amarin da ya kai ga Maurice Kamto yin murabus daga jam'iyyarsa ta MRC.

Maurice Kamto dan adawa a zaben Kamaru
Maurice Kamto dan adawa a zaben KamaruHoto: DW/E. Topona

 

Tsayar da Maurice Kamto da jam'iyyar MANIDEM ta yi na zuwa bayan cece kuce da aka jima ana yi tsakanin yan siyasar Kamaru bangaren jam'iyya masu mulki da yan adawa yan kwanakinan, har ma da masana harkokin shari'a kan takarar Maurice Kamto domin jam'iyyarsa ta MRC ba ta shiga zaben 'yan majalisa na 2020 ba, bisa dalilai na rashin kawo sauyi kan kundin zabe da kuma rashin taimakawa wajen kawo karshen rikicin sashin renon Inglishi wanda a halin yanzu babu abin da ya canza ga bukatunsa.

Maurice Kamto yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Yaounde a ranar Asabar da ta gabata ya yi wa yan jarida karin haske akan ficewarsa daga jam'iyyarsa ta MRC zuwa jam'iyyar Mouvement africain pour la nouvelle indépendance et la démocratie wato (Manidem)

Karin Bayani: Bayan shekaru 43, Biya ya nemi hadin kai don magance matsalolin Kamaru

Magoya bayan Maurice Kamto dan adawa a zaben KamaruHoto: DW/M.Mefo

Ko da kuwa wasu daga cikin magoya bayan Paul Biya kamar  karaministan shari'a kuma shugaban jam'iyyar PADDEC Jean De Dieu MOMO ya ce Maurice Kamto ya yi amai ya lashe saboda jiya ya kalubalanci tsayar da ranar zaben shugaban da Paul Biya ya yi ya ce ba bisa ka'ida ba, amma sai gashi yau shi ne kuma zai tsaya takarar.

'Yan Kamaru da dama sun nuna farin cikinsu dangane da takarar Maurice Kamto wanda ake ganin shine ya dace ya kalubalanci Paul Biya a wannan zaben.

A wannan Litinin 21 ga watan Yuli da misalin karfe 12 na dare ne, hukumar zabe za ta tsayar da karbar takardar yan takara, ranar 22 ga wannan wata, hukumar za ta gabatar da sunayen yan takara da suka cika ka'idojin shiga zabe, ga wadanda kuma aka yi watsi da takardunsu suna iya shigar da kara gaban kotun tsarin mulkin kasar. A halin yanzu yan takara 25 ne hukumar zabe ta yi rejista.