SiyasaJamus
Isra'ila: Jam'iyyun adawa sun kulla kawancen kafa gwamnati
June 3, 2021Talla
Idan har kawancen ya kai ga samun sahalewar majalisar dokoki, jam'iyyun siyasar za su maye gurbin gwamnatin Firaminisa Benjamin Netanyahu da ke kan karagar mulki fiye da shekaru 10. Naftali Bennett na jam'iyyar Larabawan Isra'ila mai ra'ayin rikau ne dai ya sauya al'amurran, kana kuma shi ne ake hasashen zai kasance sabon firaministan Isra'ila har na tsawon shekaru biyu, a karkakshin tsarin karba-karba da sabon kawancen ya cimma a jiya kafin mika jan ragamar ga jam'iyyar Yaïr Lapid. A zaben 'yan majalisun dokokin da yagabata, Mista Lapid da tsohon mai gabatar da shirye-shirye ne a talabijin, ya samu kujeru 17, inda yake biye da abokiyar hamayarta Likoud ta Benjamin Netanyahu.