1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan adawa sun janye daga shiga taron kasa

Suleiman Babayo AH
February 23, 2024

Yan takarar shugaban kasa 16 a Senegal sun kawar da yuwuwar shiga tattaunawa ta kasa.

Senegal, Dakar | Shugaba Macky Sall
Shugaba Macky Sall na SenegalHoto: Sylvain Cherkaoui/AP/picture alliance

Gungun 'yan takara 16 da ke neman shugabancin kasar Senegal a zaben da aka jinkirta sun kawar da yuwuwar shiga taron tattaunawa ta kasa da Shugaba Macky Sall ya tsara, taron da shugaban ya ce shi zai saka ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasar. Tun farko an tsara gudanar da zaben cikin wannan wata na Febrairu kafin shugaban kasar ya sanar da jinkirtawa.

Haka kungiyoyin fararen kimanin 40 na kasar ta Senegal sun kawar da batun shiga wannan tattaunawa ta kasa. Duk bangarorin sun bukaci Shugaba Macky Sall ya saka sabuwar ranar zabe domin mika mulki zuwa lokacin karewar wa'adinsa ranar 2 ga watan Afrilu.