'Yan adawar Kenya sun ce mutane 100 sun mutu
August 12, 2017Talla
Bayyana shugaba Uhuru Kenyatta na kasar a matsayin wanda ya lashe zaben ranar Talata dai ba ta yi wa bangaren adawar kasar dadi ba. Akwai ma wasu bayanan da ke nunin cewa an sami asarar rayuka a hargitsin na Kenya, jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben da yammacin ranar Juma'a.
Kungiyar kare hakkin bil adama a kasar ta ce tana da alkaluman mutane 24 da suka mutu, galibinsu a Nairobi babban birnin kasar. Bangarorin adawar da suka bayyana zaben da zama haramtacce sun dora alhakin kashe-kashen a kan jami'an 'yan sanda, wadanda suka ce suna aiki ne son ransu.