'Yan adawa a Kwango na yin tirjiya
December 27, 2017Talla
Jam'iyyar adawar dai ta ce an yi kwaskwarimar ne domin cimma burin jam'iyya mai mulki ta Shugaba Joseph Kabila. Kakakin jam'iyyar adawar Christophe Lutundula ya nunar da cewa kwaskwarimar ta hana wasu da za su iya taka rawar gani wajen tsaya wa takara da Shugaba Kabila tsayawa takara, a yayin zabukan da za a gudanar a ranar 23 ga watan Disambar shekara mai zuwa. A baya dai an amince da gudanar da zaben a karshen wannan shekara ta 2017 da muke ciki bayan cimma yarjejeniya da 'yan adawa, kafin daga bisani a dage shi zuwa karshen shekara mai zuwa.