'Yan adawar Siriya ba za su je taron Sochi ba
January 27, 2018Talla
Yahya al-Aridi me magana da yawun 'yan adawar ya bayyana haka ne a karshen kwanaki biyu bayan tattaunawar da aka yi tsakanin bangaren gwamnatin ta Siriya da 'yan adawa karkashin sa ido na Majalisar Dinkin Duniya, wacce ta ce ba ta kammala shiri ba na ko za ta shiga taron da za a yi a Sochi ba.
Kasashen Yamma dai da wasu na Larabawa na kallon taron na Sochi a matsayin wani yunkuri na samar da shirin zaman lafiya da ka iya dusashe tauraron shirin MDD da ke neman kafa ginshiki na shirin da zai kawo zaman lafiya me dorewa a kasar ta Siriya baki daya, bayan kwashe shekaru na yakin basasa da ya jawo asarar dubu daruruwan rayuka na mutane da tilasta miliyoyi kauracewa muhallansu.