1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawar Siriya na ƙara matsa ƙaimi ga ƙasashen duniya

August 29, 2013

Duk da saɓannin da ke tsakanin 'yan adawar sun haɗa kansu domin ƙalubalantar gwamnatin Bashar al-Assad.

©Christophe Petit Tesson/MAXPPP - 24/07/2013 ; PARIS ; FRANCE - Le president de la republique recoit Ahmad AL Assi Al Jarba, president de la Coalition nationale de l'opposition syrienne CNS. Ahmad AL Assi Al Jarba president of the Syrian National Coalition SNC after a meeting with French president at Elysee palace in Paris on July 24, 2013.
Ahmad al-Dscharba Präsident Syrische Nationalkoalition Besuch in ParisHoto: picture-alliance/dpa

Ƙungiyar 'yan adawa na ƙasar Siriya na ƙara jan hakalin ƙasashen duniya domin su gaggauta ɗaukar mataki a kan gwamnatin Siriya bayan hare-haren makamai masu guba da dakarun gwanmnatin suka ka kai a kusa da birnin Damascus a yau jaogoran ƙungiyar ta 'yan addawa ya isa a Faransa.

Kiran 'yan addawar ga shugabannin duniya domin su hukunta Siriya

Da ya ke yin magana da manema labarai bayan ya gana da shugaban Faransa a Ahmad Jarba jagoran ƙungiyar 'yan adawar na Siriyar ya ce suna buƙatar Faransa da sauran ƙasashen duniyar da su gaggauta ɗaukar mataki a kan Siriya domin fara kai farmakin.

Francois HollandeHoto: Reuters/Kenzo Tribouillard/Pool

Ya ce : '' Muna yin A llah wadai da hare-haren makamai masu guba mun yi kira ga ƙasashen duniya da su afkawa Siriya kana kuma a gurfanar da shugaba Assad a gaban kotun duniya a kan laifukan da ya aikata.''

A sa'ilin da ya ke ba shi ammsa shugaban Faransar Francois Hollande ya yi gargaɗin da a bi hanyoyin sulhu wajen kawo ƙarshen rikicin, tare da yin kira ga ƙasashen duniya da su guji fitina ta hanyar jingirta wa ga yunƙurin binciken da mayan jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya ke ci gaba da yi a Siriyar sannan kuma ya ƙara da cewar.

Ya ce : ''Na yi imani da halin da al'ummar Siriya suke ciki na wahalolin da kuma raɗaɗin da suke fama da shi, an kashe kusan mutun dubu ɗari a faɗan tun da aka fara shi, amma duk da haka muna fatan za a bi hanyoyin diflomasiya domin kawo ƙarshen tashin hankali.''

Rashin zutuwa tsakanin ƙasaShen a Kwamitin sulhu na MDD

A wani zaman da kwamitin sulhu na MDD ya yi a jiya a ƙudirin Ingila ta gabatar na tilasta ɗaukar matakin soji don kare fara hula. Rasha da China sun hau kujerar naƙi a kan batun yayin da a yau shugaban ƙasar Ingila David Cameron zai bayyana a gaban majalisar dokokin ƙasar domin samun amanarta.

Hoto: REUTERS/SANA

Gwamnatin Rasha da Iran sun yi kashedin cewar ɗaukar matakin zai saka yankin ciki wani bala'i wanda ba a san irin abin da zai biyo baya ba,to amma Majid Makous wani ƙusa a ƙungiyar 'yan addawar ya ce kada ƙasashen duniyar su yi fargaba.

Ya ce : ''China ko Rasha har gobe har jibi har gata ba za su amince da ƙudirin na MDD a kan gwamnatin Bashar Al Assad ba. Amma Amirka da Fsaransa a Ingila sun tabbatar da cewar Assad ya yi amfanin da makamai masu guba a kan farar hula abin da ya saɓama dokar ƙasa da ƙasa ya ce suna iya ɗaukar matakin soji a kan siriya ba tare da amincewar Majalisar Ɗinkin Duniyar ba.''

Yanzu haka dai jama'a na ci gaba da yin ƙaura daga ƙasar ta Siriya don zuwa ƙasashe makofta saboda fargaban kai hare-hare ta jiragen sama. Yayin da wasu ke zuwa a cikin bankuna wajen ɗibar kuɗaɗe, kana wasu waɗanda ba su da niyar ficewa daga ƙasar suke ci gaba da yin ceffane a kasuwani don kasancewa cikin shirin ko ta kan kwana.

Daga ƙasa za a iya sauraron rahoton da wakilinmu na Masar Mahamud Azare Yaya ya aiko mana dangane da halin da ake ciki a Siriya, haɗe da rahoton da Halima Balaraba Abbas ta rubuta mana dangane da nazarin da ƙwararru suke yi a kan taƙaddamar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu