'Yan adawar Siriya za su shiga tattaunawa
November 24, 2017Wata sanarwa da kungiyoyin suka fitar na cewa za su aike da wakilai 50, da za su halarci taron Majalisar Dinkin Duniya kan zaman lafiya da zai gudana a birnin Geneva.
Matakin kungiyoyin ya zo ne yayin da suke ganawa a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, da nufin cimma matsaya gabannin ganawa da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad a ranar 28 ga watan Nuwamba.
Cimma shawo kan kungiyoyin Siriyar ya samu nasara ne a kokarin masu shiga tsakanin na kasa da kasa, da ke kokarin kwantar da wutar rikici tsakanin 'yan adawa da bangaren gwamnati.
A baya dai MDD ta sha shirya tattaunawa da bangarorin biyu amma yana rugujewa. Yakin basasa a Siriya ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula sama da dubu 330,000, tare da tilasawa miliyoyin 'yan kasar tserewa matsugunansu.