Yan adawar Yemen sun shirya bikin farin ciki
June 5, 2011Talla
Waɗanda ke adawa da manufofin gwamnatin Ali Abdallah Saleh na Yamal sun bayyana cewar za su ɗauki dukkan matakan da suka wajaba, domin hana shugaban dawowa gida bayan karɓan magani a wani asibiti na ƙasar Saudiyya. Suna masu danganta fitar da shi daga ƙasar da wani muhimmin mataki da zai kawo ƙarshen so toka sa katsi da ake yi da nufin raba shi da madafun iko. Ɗaruruwan mutane ne dai suka fantsama akan titunan birnin Sana'a domin nuna farin cikinsu da kai shugaba Saleh da ya ji rauni da kuma iya da maƙarrabansa wajen ƙasar domin jiyya. Ya zuwa yanzu dai ba a san wanda ke riƙe da ragamar mulki ba, kasancewar shugaba saleh bai miƙata ga mataimakinsa kamar yadda dokokin ƙasar suka tanada ba. Sai dai kakakin jam'iyar da ke kan karagar mulki a Yemen wato Tarek El Chami ya bayyana ma tashar telebijin ta Al arabiya cewar nan da kwanaki ƙalilan shugaba zai dawo gida domin ci gaba da gudanar da harkokin mulki. Rikici tsakanin Bangaren gwamanti da kuma mayanƙan sa kai na ƙabilun ƙasar na ci gaba da ƙamari tun bayan wargajewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka cimma. Mawallafi:: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Yahouza Sadissou Madobi