1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: 'Yan Afirka ba sa bukatar visa

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 3, 2025

Shugaban Ghana mai barin gado Nana Akufo-Addo ya bayaana cewa, daga farkon wannan shekara ta 2025 duk wanda ke dauke da Fasfo din Afirka zai shiga kasar ba tare da takardar izinin shiga ba wato visa.

Ghana | Nana Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana mai barin gado Nana Akufo-AddoHoto: Francis Kokoroko/REUTERS

Shugaban Ghanan mai barin gado Nana Akufo-Addo ya bayana hakan ne, yayin jawabinsa ga kasa na karshe kafin ranar shida ga wannan wata na Janairu da zai mika mulki ga sabon zababben shugaban kasar John Dramani Mahama da ya lashe zabe a watan Disambar bara. Wannan matakin da Ghanan ta dauka dai, na zaman wani tafarki na gaba ga tattabatar da tsarin kasuwanci mara shinge da kasashen Afirkan ke son dabbaka wa.