1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan al-Shabaab sun kai hare-hare a Kenya

Mouhamadou Awal BalarabeJune 14, 2015

Mutane 13 sun rasa rayukansu a Kenya a wata gwabzawa da aka yi tsakanin sojoji da kuma masu kaifin kishin addini na al Shabaab a yankin Arewa maso gabashin kasar.

Hoto: Getty Images/AFP/M. Abdiwahab

Wannan fada ya faru ne sakamakon kutsawa da 'yan bindiga na al-Shabaab suka yi sansanin Baure na sojojin Kenya tare da mamaye garin Lamu da ke da iyaka da kasar ta Kenya da kuma Somaliya.

kafafen yada labarai sun ruwaito cewa daga cikin wadanda suka rigamu gidan gaskiya har da 'yan bindiga 11. Sannan kuma rundunar sojojin Kenya ta yi ikirarin kwato makamai da damai daga hannu mayakan al-Shabaab.

Wannan ya zo ne shekara guda bayan jerin hare-hare da 'yan al-Shabaab suka kai garin Mpeketoni da kewaye inda suka kashe mutane fiye da 100 da nufin tilastawa gwamnatin ta Kenya janye sojojinta daga Somaliya. Sannan kuma a watan Afirilu ma dai tsagerun na Somaliya sun kai hari jami'ar Garisa inda suka kashe mutane 148 galibinsu dalibai.