'Yan Aljeriya sun fara yunƙurin hamɓarar da shugabansu
February 12, 2011'Yan sandan ƙasar Aljeriya sun yi amfani da ƙarfi wajen tarwatsa gungun mutane da ke da niyar gudanar da zanga-zanga ƙin jinin gwamanti, makamancin na ƙasashen Tunisiya da kuma na Masar da ta yi sanadiyar hamɓarar da shugabannin waɗannan ƙasashe daga karagar mulki. Ɗaruruwan 'yan sanda kwantar da tarzoma cikin ɗamarar yaƙi ne ke aka baza birnin Algers, domin murƙushe duk wani bore na nuna adawa da manufofin gwamnatin Abdel Aziz Bouteflika.
Shugabannin jam'iyun siyasa da na ƙungiyoyin ƙodago da na ƙungiyoyin da suka himmatu wajen kyautata halin rayuwar talakawa ne suka shirya wannan gangami, da nufin tilasawa gwamanti kyautata halin rayuwar talakawa, tare da neman kawo ƙarshen salon mulki sai madi ka ture da shugaba Boutefleki ke gudnarwa.Hukumomin Aljeriya sun haramta wannan gangami saboda a cewarsu ta yi karar tsaye da dokar ta ɓaci da aka kafa tun shekaru 19 da suka gabata, wacce kuma ke haifar da guna gunin al'uma.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu