'Yan bakwai na PDP sun juya wa Jonathan baya
November 26, 2013.Awoyi kusoshin sabuwar PDP suka shafe suna taro kafin su fitar da sananrwar da shugaban bangaren Alhaji Kawu Baraje ya karanta. A cikinta dai suka sun yi imanin cewa mafita daya ta rage idan ana so a ceto demokaradiyar Najeriya: ita ce hada kai domin yin zaman aiki tare da masu adawar APC. Da ma dai taron ya samu halartar jiga- jigai na sabuwar PDP da masu zawarcinsu na APC. A cewar gwamnan jihar Adamawa Murtala Hamman Yero Nyako da ke zama jigo a cikin sabuwar PDP, taron ya tanadi jerin matakai na ganin nasarar shunfuda sabon babi a cikin tarihi na tsarin demokaradiyar kasar ta Nejriya.
Ana danganta matakin 'yan bakwai da rigakafin
Sabon matakin dai daga dukkan alamu na zaman bazata musamman ma a cikin fadar gwamantin kasar ta Abuja, wacce ta yi ta sa rana tana dagawa a kokarinta na sake bude taruka na sulhu da tattaunawa da 'yan tawayen 'ya'yan nata. Tuni dai da ma aka rika hasashen yiwuwar kaddamar da kora ta kai-tsaye ga jiga- jigan 'yan tawayen a wani taron jam'iyyar a ranar laraba mai zuwa. Saboda haka ne wasu ke kallon sabuwar rawar a matsayin wani yunkuri na tsorata shugaban kasar dama jam'iyyar PDP, da ke kallon fitar ta 'yan bakwai a matsayin babbar komabaya a burin da ta sa a gaba na mulkin kasar na shekaru 60.
Yaushe 'yan bakwai za su koma APC?
Sai dai a cewar Rabi'u Musa kwankwaso dake zaman gwamnan jihar kano matakin nasu bashi da nasaba da kokari na tsorata masu mulkin kasar ta Najeriya da suka yi tsayiwar gwamin jaki ga jerin bukatu takwas na 'ya'yan jami'iyyar. yarjejeniyar da aka ratabba wa hannu a gidan gwamnatin jihar kano ta bar wa sabobbin amaren 'yancin shiga cikin dakin APC a gaba daya, a duk lokacin da suke ganin hali ya yi musu daidai. To sai dai kuma 'ya'yan APC na can na taro da nufin nazarin tasirin sabbin mambobin nasu cikin jam'iyyar.
Mawallafi: Ubale Musa daga Abuja
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe