1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan bindiga a Jamhuriyar Nijar sun hallaka jami'in gwamnati

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 23, 2024

Daga cikin wadanda aka sace har da babban jami'in birnin Bilma Amadou Torda

Hoto: AFP

Wani harin 'yan bindiga a Jamhuriyar Nijar ya yi sanadiyyar mutuwar jami'in gwamnati daya, sannan suka yi garkuwa da guda biyar, sakamakon kwanton bauna da suka yi wa jerin gwanon motocin ma'aikatan, a kan hanyarsu ta dawowa daga wani rangadi a birnin Bilma na arewacin kasar.

Karin bayani:Harin ta'addanci ya halaka jami'an gwamnatin Nijar da kuma soja

Sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Nijar ta fitar ranar Asabar, ta ce lamarin ya faru ne ranar Juma'a, kuma daga cikin wadanda aka sace har da babban jami'in birnin wato Amadou Torda, amma bata bayyana sunan sauran hudun da aka yi garkuwa da su ba, kuma wani mutum daya ya samu munanan raunuka a jikinsa sakamakon harin.

Karin bayani:Sojojin Nijar sun murkushe harin ta'addanci

Har zuwa wannan lokaci dai babu wadanda suka yi ikirarin kai harin, amma sojojin Nijar din sun dukufa don zakulo maharan.

Yankin Bilma mai matukar sahara, na da nisan kilomita 1,300 da Yamai babban birnin kasar, kuma ya yi kaurin suna wajen fama da hare-haren ta'addanci da safarar makamai da muggan kwayoyi, baya ga safarar bil'adama zuwa ketare.

Ko a watan Fabarairun da ya gabata sai da maharan suka kashe sojojin Nijar 8 a yankin.