1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikice

'Yan bindiga sun halaka mutane 40 a Haiti

August 25, 2026

Akalla mutum 40 ne aka kashe bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan mutanen da suka rasa matsugunansu da ke fakewa a wata coci kusa da Port-au-Prince, babban birnin kasar Haiti.

Mazauna yankin sun bukaci shugaban 'yan sandan yankin ya yi murabus, bisa zargin cewa 'yan sanda sun gaza kare mutanen da ke samun mafaka a cocin.
Mazauna yankin sun bukaci shugaban 'yan sandan yankin ya yi murabus, bisa zargin cewa 'yan sanda sun gaza kare mutanen da ke samun mafaka a cocin.Hoto: Odelyn Joseph/AP Photo/dpa/picture alliance

Magajin garin Kenscoff ya ce maharan sun kutsa cikin sansanin da ke cocin a daren Lahadi, inda suka kashe mutane tare da jikkata wasu da dama, yayin da suka yi garkuwa da wasu. Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin wadanda suka mutu zai iya kaiwa 47, yayin da sama da 22 suka jikkata.

Karin bayani : 'Yan bindiga sun bude wuta kan jirgin MDD a Haiti

Gwamnatin Haiti ta yi Allah-wadai da harin tare da tura karin jami'an tsaro yankin. Haiti dai ita ce kasa mafi talauci a nahiyar Amurka kuma tana fama da karuwar hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai, lamarin da ya raba kusan mutane miliyan 1.5 da muhallansu.

Karin bayani : Chad za ta aike da dakaru 750 zuwa Haiti don taimakawa tsaro

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW