1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan bindiga sun halaka mutane a iyakar Benin da Nijar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 18, 2024

Maharan sun je ne a kan babura, inda suka bude wa mutanen wuta da tsakar daren Talata, kuma har yanzu ba a san dalili ba

Hoto: Rodrigue Guezodje/DW

Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba kai ga tantance su ba, sun halaka mutane 3 ciki har da soja daya, tare da raunata wani sojan, lokacin da suka kai hari kan iyakar Jamhuriyar Benin da Jamhuriyar Nijar.

Karin bayani:Benin: Martani daga 'yan kasuwar Nijar

Magajin garin Malanville Gado Guidami, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa maharan sun je ne a kan babura, inda suka bude wa mutanen wuta da tsakar daren Talata, kuma har yanzu ba a san dalili ba.

Karin bayani:Bambancin ra'ayi kan rashin bude wasu iyakokin Nijar

Jamhuriyar Benin tana da iyaka da kasashen Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso ta arewaci, wadanda suka jima suna fama da hare-haren ta'addanci na kungiyoyi masu alaka da al Qaeda da IS.