'Yan bindiga sun hallaka mutane 11 a Najeriya
August 17, 2013Talla
Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram sun hallaka mutane 11, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.
Lamarin ya faru cikin daren ranar Alhamis a garin Damboa na Jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar, yankin da ke zama tungar kungiyar Boko Haram mai gwagwarmaya da makamai. Tun cikin watan Mayu jihar ke karkashin dokar ta baci, wanda Shugaba Goodluck Jonathan ya kafa.
Hare-hare masu nasaba da kungiyar sun yi sanadiyar salwantar rayuka masu yawa, tun lokacin da kungiyar ta kaddamar da farmakin a shekara ta 2009.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh