Mutane da dama sun rasa rayukkansu a kauyukkan Sokoto
February 26, 2019Talla
A Tarayyar Najeriya akalla mutane 16 ne suka rasa rayukkansu a kauyukkan Dalijan, da Kalhu a karamar hukumar Rabah da ke Jihar Sokoto a arewacin kasar
Wannan lamarin dai ya faru ne sakamakon afkawa mazauna kauyen da wasu dauke da makamai da ake kyuatata zaton barayin shanu ne suka yi a daren Litinin, kamar yadda Anas Ghandi wani mazaunin kauyen ya shaidawa wakilinmu na Jihar Sokoto.
Yankin dai na makwabataka ne da Jihar Zamfara da yanzu hakan ke fama da hare-haren 'yan bindinga, wanda akai-akai suke yi wa kauyen na Rabah kutse. Ko a makwannin baya ma dai wasu mutane akalla 10 sun halaka a wani harbi na kan mai uwa da wabi da 'yan bindigan suka yi ta yi a kauyukan .