1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun hallaka mutane da dama a Kongo

Ahmed Salisu
February 11, 2025

Wata kungiya da ke dauke da makamai a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta afkawa wasu kauyuka da ke gabashin kasar inda mambobinta suka hallaka mutane da dama tare da yi wa mata da ma 'yan mata fyade.

Demokratische Republik Kongo | Stadt Bunia | Milizionär
Hoto: STUART PRICE/AFP/Getty Images

Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewar wani jami'an dan sanda ya ce sun gano gawarwaki mutane kimanin hamsin da biyar a cikin wasu dazuka a lardin nan na Ituri.

Baya ga kisa da kuma fyade da 'yan bindigar suka yi, wani mazaunin Lardin ya ce maharan sun kuma kwashi kayan da mutanen kauyuka suka gudu suka bari, inda suka cinnawa gidajen wuta bayan sun kammala sace-sacen.

Tuni dai mazauna yankin suka fara zargin 'yan kungiyar nan ta CODECO da kai wannan hari, sai dai ya zuwa yanzu ba wata majiya mai zaman kanta da ta tabbbatar da wannan labari.