1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun hallaka sama da mutum 20 a Zamfara

July 23, 2026

A Najeriya, akalla mutane 23 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hare-hare kan ƙauyuka biyar da ke gundunmawar Sauna a ƙaramar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal
Gwamnan jihar Zamfara Dauda LawalHoto: Dauda Lawal/Facebook

Kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, ya ruwaito jami'ai a yankin na cewa galibin waɗanda aka kashe manoma ne, yayin da wasu mutum uku da suka jikkata ke ci gaba da samun kulawa a asibiti. Har yanzu rundunar 'yan sandan jihar ba ta ce komai kan harin ba.

Hakan na zuwa ne kasa da mako guda da 'yan bindiga suka sace sama da mutum 40 a hare-haren da suka kai kauyuka 11 da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar taZamfara.

Harin na baya-bayan nan ya sake nuna yadda matsalar tsaro ke ci gaba da addabar arewa maso yammacin Najeriya, inda 'yan bindiga ke kashe mutane sannan su yi garkuwa da su domin karɓar kuɗin fansa da kuma satar dabbobi.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW