SiyasaAustraliya
'Yan bindiga sun kai hari a Australiya
December 14, 2025
Talla
Tuni aka harbe dan bindiga yayin da jami'an tsaro suka yi nasarar damke guda, hukumomin Australiya sun ayyana wannan mummunan harin da ta'addanci.
A cewar kwamishinan 'yan sanda na jihar New South Wales akalla mutane 29 ne aka tabbatar sun samu raunuka daga cikinu har'da jami'an tsaro biyu.
Da yake jawabi a inda wannan al'amari ya faru, gwamnan jihar ya ce manufar harin da kuma makaman da aka yi amfani da su ba makawa hari ne na ta'addanci da kuma tsanar Yahudawa.
Firaministan Austaraliya ya yi tir da wannan harin inda ya mika sakon ta'ziyarsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su.
Austiraliya ta fuskanci karuwar jerin hare-haren a majami'u da gine-gine da motoci tun farkon yakin Isra'ila a Gaza a watan Oktoban.