'Yan bindiga sun kai hari a kan masu ciwon Ebola
August 17, 2014Talla
Wani jami'in na ƙungiyar ma'aikatan kiwon lafiya na ƙasar, George Williams ya ce daga cikin marasa lafiya guda 29 da suka karɓa a asibitin na wucin gadi ,17 sun tsere sakamakon hare-haren.
Masu jinyar waɗanda aka tattarasu a cikin wata makarantar waɗanda 'yan uwansu suka kai su da ƙarfi da yaji domin a bincikesu. Ana ba su kulawa ta farko kafin a isar da su a asbiti bayan da aka gano cewar suna ɗauke da cutar ta Ebola. Tun da farko a kwanaki huɗun da suka wuce tara daga cikinsu sun mutu yayin da a ranar Asabar wasu uku suka kwanta dama. Ya zuwa yanzu ba a san dalilan da ya sa maharan waɗanda galibi matasa ne suka kai harin ba a cibiyar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu