'Yan bindiga sun kai hari ga tawagar Sarkin Kano
January 19, 2013Sama da mutane Biyar ne akayi ittifaƙin sun rasu wasu kuma suka sami raunuka lokacin da wasu mutane ɗauke da bindigogi suka kai farmaki ga tawagar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero,lokacin da ya ke dawowa akan hanyarsa ta tafiya gida bayan halartar wani bikin saukar Alƙur'ani da akayi a wata makarantar islamiyya da ke unguwar masallacin Murtala a cikin Kano.
Wannan hari dai shine irinsa na farko da aka kai ga wani babban mai riƙe da sarautar gargajiya a jihar Kano,kuma duk da cewar ba a sami mai martaba Sarkin ba, amma an ragargaza motar da yake ciki wanda yayi sanadiyyar mutuwar direbansa, da kuma raunata dogarinsa dake kula da lafiyarsa sai kuma wasu fadawa ukku,da suka rasu da wasu kuma da suka sami rauni.Cikin waɗanda suka sami rauni a yayin harin, harda wasu manyan 'ya'yan Sarkin Biyu da suka haɗa Nasiru Ado Bayero wanda shine hakimin Tarauni.Wani ma aikaci dake cikin ayarin sarkin lokacin da harin, ya bayyana abin da ya faru.
Tuni dai aka kai gawarwakin waɗanda suka rasu da kuma waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Murtala da asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, inda mutane da dama suka je domin duba yanuwansu da suka je taron, kuma ba a ga dawowarsu gida ba.Mubarak Sayyadi magidanci ne da muka iske a asibitin Murtala ya bayyana cewar yazo ne domin neman iyalinsa, waɗanda suma sun halarci taron,kuma ba a ga komawarsu gida ba.
Shima kantoman ƙaramar hukumar Kumbotso da ke jihar ta Kano ya rasa ransa, yayin wannan farmaki lokacin da ya yi ƙoƙarin gujewa farmakin a cikin motarsa inda wasu maharan suka bishi a baya suka kuma buɗe masa wuta nan take kuma ya rasa ransa.
Alhaji Baban Ladi Satatima shine Barden madakin Kano ya bayyana matuƙar takaici bisa yadda hare-haren suka fara ɗaukar wata alƙibla ta daban.
A nasa ɓangaren gwamnan jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar jaje ga fadar mai martaba Sarkin harma ya bayyana takaici bisa faruwar wannan farmaki.
Daga fadar Sarkin dai gwamnan na Kano ya zarce ne zuwa filin jirgin saman Malam Aminu Kano dake jihar inda ya shiga jirgi zuwa ƙasar Indiya.
Mawallafi: Nasir Salisu Zango
Edita:Yahouza Sadissou Madobi