Burkina Faso: Yan bindiga sun kashe fararen hula
May 20, 2023![Mutum sama da 30 'yan bindiga suka kashe a wannan makon a Burkina Faso](https://static.dw.com/image/62173989_800.webp)
A kasar Burkina Faso da ke yankin Sahel, fararen hula kimanin goma sha biyu ake zargin wasu mayaka masu da'awar jihadi da kashewa a wani hari da suka kai a yankin yammacin kasar da ke iyaka da kasar Mali.
Wani ma'aikacin gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, maharan sun zo da yawansu dauke da muggan makamai, sun afka wa kauyen mai suna Kie a daren Jumma'ar da ta gabata, in da suka yi wa kauyen kawanya kafin daga bisani sun cinna masa wuta, da wuya a iya tantance adadin mutanen da ya ce, an kashe ganin da yawa sun ji munanan rauni baya ga asarar dukiyar da aka tafka a harin.
Kazamin harin na zuwa ne, kwana guda bayan wani makamancinsa da 'yan bindiga suka kai da ya salwantar da rayuka ashirin a kasar da yanzu haka ke fada da ayyukan 'yan ta'adda.