1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe gomman mutane a Taraba

October 25, 2026

Alkalumman wadanda suka mutu sakamakon harin ’yan bindiga a garin Binnari na jihar Taraba da ke Najeriya ya karu zuwa mutum 50, bayan gano karin gawawwaki.

Nigeria Goniri 2026 | Nigerianischer Soldat bewacht ein Dorf im Nordosten des Landes
Hoto: AFP

Ana zargin wasu 'yan bindiga da afka wa garin Binnari na jihar Taraba a kan babura ranar Juma'a, inda suka kashe mutane tare da wawashe shaguna. Sai dai a ranar Asabar, wadanda suka tsira suka ce mutane 20 ne suka mutu bayan gano karin gawawwaki, kamar yadda wani mazaunin garin Abdullahi Zakari ya bayyana. Zakari ya shaida wa AFP cewa mazauna garin da dama, ciki har da mata da yara, sun gudu zuwa kogin domin tsere wa 'yan bindigar, amma wasu sun nutse yayin kokarin tsira.

Karin bayani: Neman mafitar matsalolin tsaron arewacin Najeriya

Yankin arewa maso gabashin Najeriya ya dade yana fama da rikicin kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai. Sai dai jihar Taraba, tana kuma fuskantar hare-haren kungiyoyin 'yan bindiga masu neman kudi, maimakon yada wata akida. Kungiyoyin kan kai hare-hare kauyuka tare da tilasta wa manoma da masu hakar ma'adinai biyan haraji musamman a yankunan da hukumomin gwamnati ba su da karfin iko sosai.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW