1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Zamfara wasu Mahara sun hallaka Hakimi

July 7, 2018

Yayinda rikicin jihar ta Zamfara ke kara yin kamari a yanzu ta kai ga hallaka basarake duk kuwa da matakin da hukumomi ke cewa suna dauka don inganta tsaro.

Nigeria Demonstration gegen Gewalt im Bundesstaat Zamfara
Hoto: DW/Yusuf Ibrahim Jargaba

Rahotanni da ke fitowa daga yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, na cewa wasu 'yan bindiga da ba'asan ko su waye ba ya zuwa yanzu, sun bindige har lahira Alhaji Ibrahim Madawaki, hakimin Kucheri da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. 

Rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara ta tabbatar da afkuwar lamarin ta bakin kakakinta SP Shehu Muhammad kamar yadda ya yi wa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba karin bayani. Jihar Zamfara dai na ci gaba fuskantar hare-haren 'yan bindiga kusan ko wane mako, lamarin da ke sanadiyar rasa rayukan al'ummomin da basu ji ba su gani ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW