1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 13 a Zamfara

August 10, 2025

Maharan sun yi wa jami'an tsaron kwanton bauna ne bayan kokarin da suka yi na kwace mutanen da aka sace daga kauyukansu.

Daga cikin jami'an tsaron da aka halaka har da 'yansanda biyu
Daga cikin jami'an tsaron da aka halaka har da 'yansanda biyuHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Wasu 'yan bindiga sun halaka jami'an tsaro 13, ciki har da ‘yan sanda biyu da ‘yan sa-kai 11, a jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

Wannan harin wani sabon tashin hankali ne a yankin, kamar yadda mazauna suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Lahadi.

An sace sama da mutane 60 a Zamfara

'Yan bindiga sun dade suna addabar al'ummomi a arewa maso yamma da tsakiyar Najeriya, sannan suna kai hare-hare kan kauyuka da sace mutane da kona gidaje.

A cewar majiyoyin, ‘yan bindigan masu yawan gaske sun mamaye kauyen Adabka da ke Bukkuyum a daren Juma'a, sannan suka sace wasu mazauna kauyen tare da tserewa da su zuwa cikin daji.

Najeriya: 'Yan bindiga sun kashe mutane 33 a jihar Zamfara

Har ila yau, sun yi kwanton bauna suka bude wuta kan tawagar ‘yansanda da ‘yan sa-kai da ke bin su domin ceto wadanda aka sace.