'Yan bindiga sun kashe mutane 200 a Najeriya
February 5, 2026
Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar yankin Mohammed Omar Bio, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa adadin mutanen da 'yan bindigar suka kashe a kauyukan Woro da Nuku ya kai mutum 162, wanda ke kasancewa hari mafi muni da aka gani a yankin.
Karin bayani:Harin da aka kai a Woro na jihar Kwara ya kashe mutane 67
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana kaduwarsa dangane da wannan mummunar hari na ranar Talata, wanda ya bayyana shi a matsayin dabbanci.
Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe mutane a coci a Najeriya
Sakataren Kungiyar Red Cross a jihar ta Kwara, Ayodeji Emmanuel Babaomo, ya ce har ya zuwa wannan lokaci sun kasa isa yankin domin kai agajin gaggawa, sakamakon rashin kyawun hanya da kuma tazarar da ke tsakanin yankin da babban birnin jihar Ilorin. Kauyukan na Woro da Nuku dai na kusa da kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin.