An kashe mutane a wata majami'a a Kwara
November 19, 2025Rahotannin cikin gida na cewa maharan sun kutsa cikin majami’ar Christ Apostolic da ke karamar hukumar Ekiti da makamai a yayin ibadar yamma, wasu bidiyon d ake yawo a shafukan sada zumunta na kyamarar sirri na CCTV ya nuna yadda maharan suka gigita mutane.
Bidiyon ya nuna an katse masu hidimar cocin da harbin bindiga, kuma an ji yara suna kururuwa a waje. An ga wani mutum dauke da makami yana fatattakar masu ibada, yayin da wasu ke satar kayan mutane.
“Da taimakon ’yan banga, wadan da suka mayar da martani ga maharan, lamarin da ya sa ‘yan bindigar suka tsere zuwa cikin daji,” in ji rundunar ‘yan sandan jihar Kwara a wata sanarwa da ta fitar cikin dare.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci a tura karin jami'an tsaro cikin gaggawa don kare sauran wuraren a yankin, kamar yadda wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa ya fitar a safiyar Laraba.
Jihar dai ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan watannin nan, lamarin da ya sa shugaban Najeriya, Bola Tinubu a watan Oktoba ya tura jami’an soji domin fatattakar ‘yan bindiga a dazuzzukan jihar.
Harin na zuwa ne bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump a farkon watan Nuwamba ya yi barazanar daukar matakin soji kan abin da ya yi ikirari ana yi wa kiristocin Najeriya kisan gilla, ikirarin da gwamnatin Najeriyar ta yi watsi da shi.