1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe mutane a Kaduna

June 10, 2022

Wasu mahara dauke da muggan makamai, sun salwantar da rayuka a wani hari da suka kai kan mazauna yankuna karkara a jihar Kaduna mai fama da fitintinu a Najeriya.

Nigeria | Schulkindern entführt
Hoto: AP/picture alliance

Sama da mutum 30 ne rahotanni ke tabbatar da mutuwar su a wani hari da wasu suka kai wasu kauyukan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Hukumomi a jihar sun ce maharan wadanda ke cikin ayari bisa babura sun afka wa kauyen Dogon Noma ne da Unguwar Sarki da Unguwar Maikori, dukkanin su da ke yankin karamar hukumar Kajuru inda baya ga kisan mutanen sun kone gidaje da dama.

Cikin 'yan watannin da suka gabata ne ma dai wasu maharan suka kashe sama da mazauna yankunan karkara mutum 100 tare da wasu gomman 'yan banga da ke samar da tsaro.

Haka ma cikin makonnin da suka gabata, wasu 'yan bindigar sun afka wa wani jirgin kasa a tsakanin Abuja da Kaduna, inda sukayi awon gaba da mutane da dama.